Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Cutar Corona ta sa an dakatar da ‘yan kallo shiga wajen wasanni

Published

on

 

Hukumomin gudanar da kwallon kafa a kasar Andalus, wato Spain sun tabbatar da cewar za’a fafata wasannin manyan kungiyoyin rukuni na daya da na biyu, na tsawon mako biyu ba tare da ‘yan kallo ba sakamakon barazanar yaduwar cutar Corona virus.

Wasan Eibar da Real Sociedad,  za ayi shi ba  tare da ‘yan kallo sun shiga ba haka kuma rahotanni sun tabbatar da cewar  hukuncin dakatar da ‘yan kallon zai fara tun daga yau Talata.

Hukumar  ta La liga, ta ce ta dau matakin ne biyo bayan shawarar da Ma’aikatar lafiya ta kasar ta bayar, a ta bakin shugaban sashen lafiya na yankin Catalonia, Joan Guix.

Labarai masu alaka.

Yadda wasannin zakarun nahiyar Turai ke gudana

Dalilan dakatar da wasanni a birnin Tokyo

Zuwa yanzu haka wasu manayan wasanni da suka hada da,  wasan Barcelona da Napoli a gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai, da wasan Sevilla da As Roma sai wasan Getafe da Inter Milan a gasar cin kofin Kalubale, na nahiyar Turai wato Europa league, da wasan Paris Saint German da Borussia Dortmund, a gasar zakaru nahiyar turai, champions league duk za’a fafata su ba  ‘yan kallo.

Sai wasan Manchester United da LASK Linz ta kasar Austria,  da shima hakan ta shafe shi ba tare da ‘yan kallo.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!