Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

An dakatar da gasar Firimiyar kasar Ingila sabo da-Corona

Published

on

Hukumar shirya gasar premier ta kasar Ingila ta sanar da dakatar da gudanar da gasar firimiya  ta kasar sakamakon barazanar yaduwar cutar Coronavirus.

Hukumar  ta sanar da cewar  za’a dawo gudanar da gasar ne  ranar 04 ga watan Afrilu bana.

Ana dai zargin ‘yan wasan kwallon kafa da dama a kasar ta Engila na  dauke da kwayar cutar  mai lakabin  Covid 19.

Sanarwar, dakatarwar ta  shafi dukkanin  wasannin da ake bugawa a gasar  da karamar gasar  sai ta  mata da gasar FA.

Dakatar da gasar ya biyo bayan shawarwari da hukumar shirya gasar tayi da  likitoci wanda suka ce cigaba da gudanar da gasar ka iya haifara da hatsarin kamuwa da cutar.

Zuwa yanzu dai kasashe da dama a nahiyar turai  sun dakatar da gudanar da wasannin kwallon kafa da suka hadar da gasar Serie A ta kasar Italiya da Laliga ta kasar Spaniya sai  Bundesliga ta kasar Jamus da ligue 1 ta kasar Fransa.

Haka kuma masana kiwan lafiya a kasar sun baiwa kungiyoyi na wasanni a kasar shawarar kauracewa  duk wani taron jama’a ko kuma taro tsakanin ‘yan wasa da ‘yan kallo da kuma ziyarar baki zuwa filayen wasanni.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!