Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Ko Real Madrid za ta iya daukan Laliga?

Published

on

A makon daya gabata ne kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta samu nasarar doke kungiyar kwallon kafa ta Barcelona da ci 2-0 a wasan hamayya na kasar  Espaniya, wanda ake wa lakabi da El-clasico.

Nasarar da Real Madrid ta samu kan Barcelona da ci 2-0 ya bawa Real Madrid damar darewa saman teburin La ligar.

Sai dai a wasan wannan mako  27, Ungulu ta koma gidanta na tsamiya bayan da Madrid din ta yi rashin nasara a hannun Real Betis da ci 2-1, yayin da Barcelona ta doke Real Sociedad  da ci 1-0 wanda hakan ya bawa Barcelona damar komawa matakin farko da maki 58, Madrid ke biye mata da maki  56.

LABARAI MASU ALAKA

Shin ko Atletico Madrid za ta samu nasara kan Liverpool?

Madrid na fuskantar barazanar ficewa daga Champions League

Hukuncin kotu ba zai hana mu lallasa Madrid ba – Guardiola

A wasanni hudu da Real Madrid ta buga a kwanakin nan nasara daya ta samu tak wanda haka ba karamin koma baya bane ga kungiyar.

Levente 1 Real Madrid 0

Manchester City 2 Real Madrid 1 (Gasar cin kofin zakarun nahiyar turai)

Real Madrid 2 Barcelona 0

Real Betis 2 Real Madrid 1

Tun a kakar wasanni ta shekarar 2016-2017 Madrid bata kara lashe gasar ta La Liga ba, duk da cewa cikin wannan shekaru ta lashe gasar cin kofin zakarun nahiyar turai har sau uku a jere.

Magoya bayan kungiyar ta madrid na ganin cewa wannan rashin nasara da kungiyar ke samu na da alaka da rashin tsayayyen dan wasan gaba mai zura kwallo, kasancewar har yanzu kungiyar ta kasa samun dan wasan da zai maye gurbin, jagoranta a baya Cristiano Ronaldo wanda ya koma kungiyar kwallon kafa ta Junventus da ke kasar Italiya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!