Labarai
A ƙalla mutane kusan miliyan 3 rikici ya raba da gidajensu a Najeriya – majalisar ɗinkin duniya
Hukumar kula da ƴan gudun hijira ta majalisar ɗinkin duniya (UNHCR) ta ce a ƙalla mutane miliyan 2 da dubu ɗari tara ne rikice-rikice da ke faruwa a Najeriya ya raba da gidajensu.
A cewar hukumar ta UNHCR akwai kuma mutane da ke zaune a sansanonin ƴan gudun hijira da suka kai 70, 000.
Babban jami’in hukumar da ke kula da yada labarai ta ƙetare Roland Schoenbauer da kuma jami’in yaɗa labaran hukumar anan Najeriya Gabriel Adeyemo sune suka bayyana haka yayin zantawa da manema labarai a shalkwatar hukumar da ke Lagos.
Sai dai hukumar ta yabawa Najeriya sakamakon yadda ta ce tana iya kokarinta wajen kula da ƴan gudun hijira wadanda suka shigo Ƙasar nan daga ƙasashe makwabta don neman mafaka.
Ya ce abin alfahari shine ganin cewa ƴan gudun hijira ana basu damar yin aiki ko neman ilimi da kuma kula da lafiya kamar yadda ƴan kasa ke da wannan dama.
Saboda haka hukumar ta bukaci ƙasashe mawadata da su taimaka wajen samar da isassun kudade da za ta ci gaba da gudanar da ayyukanta ba tare da samun matsala ba.
You must be logged in to post a comment Login