Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A ƙarshen shekara: Buhari ya sanya hannu kan kasafin kuɗin 2022

Published

on

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kuɗin shekarar 2022 da kuma ƙwarya-ƙwaryar kasafin kuɗi na 2021.

Shugaban ya sanya hannu a ranar juma’a a fadarsa tare da shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, da na majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, da sauran mambobin majalisar zartarwa ta tarayya.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan sanya hannun shugaban ƙasar ya ce jimillar kasafin kuɗin shekarar 2022 ya kai Naira tiriliyan 17 da biliyan 127, wanda aka samu ƙarin Naira biliyan 735.85 bisa kudurin farko da aka gabatar da Naira tiriliyan 16 da biliyan 391.

Shugaban ya bayyana cewa ƙarin Naira biliyan 186 da biliyan 53 ya samu ne bayan da ministar kuɗi, kasafi da tsare-tsare Hajiya Zainab Ahmad ta mika buƙatar hakan ga majalisar dokokin ƙasar.

Shugaban ya sanar da cewa, a yayin da kasafin kuɗin shekarar 2023 zai kasance kasafin mika mulki ga wanda ya samu nasara, za a yi ƙoƙarin gabatar da shi da wuri kuma zai kasance matsakaici tun daga 2023 zuwa 2025.

Don haka ya buƙaci shugabannin ma’aikatu da hukumomi da su haɗa kai da ma’aikatar kudi da kasafi don ganin an cimma burin da aka saka a gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!