Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A buɗe sauran shagunan da ba na sayar da magani ba -Dilolin magani ga NAFDAC

Published

on

Wasu daga cikin ‘yan kasuwar mai Ƙarami Plaza da ke yankin Malam Kato a Kano, sun bukaci hukumar kula da ingancin abinci da magunguna NAFDAC ta buɗe sauran shagunan da ba na sayar da magani ba wanda ta kulle sakamakon saɓani da aka samu a kasuwar.

Mutanan sun bayyana hakan yayin wani taron gangami da suka gudanar a yammacin ranar Talata.

Ƴan kasuwar sun ce ba masu magani kaɗai ba ne ke kasuwanci a kasuwar ta Mai Karami Plaza, a don haka bai kamata a rufe kasuwar ba.

Sun Kuma ce yanzu haka sakamakon rufe kasuwar da aka yi wasun su na neman su fara tagayyara.

Wakilin mu Aminu Abdu Baka Noma ya rawaito cewa, Koda suka tuntuɓi hukumar ta NAFDAC kan wannan batu, ta ce ta samu koken nasu kuma ta bayar da damar aje a gudanar da bincike domin tantance shagunan da ba na sayar da magani ba don ci gaba da kasuwanci.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!