Connect with us

Siyasa

A hukumance Injiniya Abba Kabir Yusuf ya koma jami’iyyar (NNPP

Published

on

Tsohon dan takarar gwamnan Kano a jami’iyyar PDP a zaben 2019 Abba Kabiru Yusuf ya sanar da komawa sabuwar jami’iyyar NNPPP daga jami’iyyarsa ta PDP.

Wannan na zuwa ne bayan wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudanar a ranar Lahadi mazabarsa ta Diso dake karamar hukumar Gwale a nan Kano.

Hadimi namu samman ga Abba Kabiru Yusuf ne ya sanar da hakan a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Lahadi.

Cikin wadanda suka halarci taron sauya shekar Abba Gida-Gida sun hada da mataimakinsa Kwamrade Aminu Abdussalam da kuma shugaban jami’iyyar ta NNPP a nan Kano Haruna Umar Dogowa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!