Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

A jiya mutum 15 ne suka kamu da cutar Corona a Kaduna

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El rufa I ya bayyana cewa, an sami nasarar sallamar mutum daya bayan daya warke daga cutar COVID 19.

Malam Nasiru El rufa I ya bayyana hakan ne a shafin sa na Tweeter a jiya kan yawan wadanda suka kamu da cutar corona a jiya da kuma wadanda aka yi wa gwaji.

Ka zalika daga cikin wadanda aka yi wa gwaji 111 an sami mutum 15 dake dauke da cutar a jihar ta Kaduna,9 daga ciki sun fito ne daga yankin Arewacin jihar.

Labarai masu alaka :

Gwamnatin Kaduna ta sanya dokar hana zirga-zirga a wasu kananan hukumomi

Covid-19: An kori limamin jumu’a a Kaduna

An sassauta dokar kulle a jihar Kaduna

Har ila yau, mutum 4 daga cikin wadanda suka kamu da cutar sun fito ne daga Karamar hukumar Kubau ya yin da mutum guda daga karamar hukumar Zangon Kataf sai kuma daya daga karamar hukumar Cukun.

 

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!