Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

A karon farko cikin watanni 4 an samu raguwar masu cutar Corona – NCDC

Published

on

Karon farko cikin watanni hudu an samu raguwar masu kamuwa da cutar corona mafi karanci a kasar nan.

A jiya litinin dai mutane 143 ne kacal hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta sanar da cewa sun kamu da cutar ta covid-19.

Ya zuwa yanzu dai, jimillar wadanda suka harbu da cutar ta corona a NAJERIYA sun zarce dubu hamsin da hudu.

Sama da mako guda kenan hukumar ta NCDC ke sanar da raguwar masu harbuwa da cutar ta corona, wanda a makon jiya mutane dubu daya da dari takwas da ashirin da biyu ne kawai suka kamu da cutar ta covid-19.

Wannan na zuwa ne a lokaci guda da gwamnatin tarayya ke gargadin jihohi game da gaggawar bude makarantu, tana mai cewa, har yanzu fa, da sauran rina a kaba.

NCDC ta ce, an samu bullar cutar ce a jihohi goma sha takwas da birnin tarayya Abuja.

Jihohin sun hada da: Filato da Kaduna da Lagos da Ebonyi da Adamawa, Enugu, Katsina, Edo da kuma Kwara sai kuma birnin tarayya Abuja.

Sauran sune: Osun, Anmabra, Kano, Niger, Ogun da Benue da Borno da kuma Sokoto.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!