Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

A na sa ran Man fetur zai yi sauki kamar yadda na iskar gas yayi a yanzu- Mai Kifi

Published

on

Zauren dillalan man fetur na Nijeriya ya ce, tashin farashin litar mai da aka samu ya shafi harkokin kasuwancinsu fiye da yadda ake tunani.

Shugaban zauren shiyyar Arewa Alhaji Musa Yahya Mai Kifi ne ya bayyana hakan, yayin tattaunawarsa da Freedom Radio.

Alhaji Musa Yahya Mai Kifi ya kuma ce ‘ana sa rai nan gaba a samu saukin tsadar man fetur din a kasar nan, kamar yadda na iskar gas ya sauka.

Mai Kifi ya ce, ‘kamata ya yi gwamnatin tarayya ta samar da hanyoyi da za a bi kafin a janye tallafin man fetur din kai tsaye, ba wai a janye ba tare da samarwa kasar nan hanyar da za’a saukaka musu ba.

Rahoton:Madeena Shehu Hausawa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!