Labarai
A riƙa tausayawa talakawa –Sarkin Kano ga mahukuntan Asibitin Dala
Mai martaba sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya buƙaci mahukuntan asibitin ƙashi na Dala, da su samar da tsarin ragewa marasa lafiya raɗaɗin kuɗin magani da kuma inganta ayyukan kula da su.
Sarkin yayi wannan kira ne lokacin da ma’aikatan asibitin ƙashi na Dala ƙarƙashin jagorancin sabon shugaban asibitin Dakta Nuraddeen iIsah suka ziyarce shi a fadar sa.
Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce, akwai buƙatar hukumomin asibitin su yi la’akari da halin matsin rayuwa da aka shiga a wannan lokaci, don sauƙaƙawa al’umma.
A nasa jawabin Sabon shugaban asibitin Dakta Nuraddeen Isah, ya tarbatarwa da sarkin cewa, za su samar da sabon tsarin don ganin an taimakawa marasa lafiya, ciki har da samar da motoci don ɗauko marasa lafiya.
Wakilinmu na masarautar Kano Shamsu Da’u Abdullahi ya rawaito cewa, yayin ziyarar Dakta Nuraddeen Isah ya ce, sun horar da likitoci daban-daban domin kula da lafiyar al’umma da kuma magance fita ƙasashen ƙetare don neman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login