Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Matsin rayuwa: za mu tsunduma yajin aikin gama-gari – NLC da TUC

Published

on

Gamayyar kungiyoyin ƙwadagon Najeriya NLC da TUC sun sanar da shirin su na tafiya yajin aikin gama-gari.

Cikin wata sanarwa da suka fitar NLC da TUC, sun baiwa gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu da ta kawo ƙarshen matsalolin da ake fuskanta ko kuma su tsunduma yajin aiki a ƙasar.

Kungiyoyin sun sanar da cewa, sun bada wa’adin ne biyo bayan gaza cika alƙawarin da suka ƙulla da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu tun a ranar 2 ga watan Oktobar 2023, bayan cire tallafin mai fetur.

NLC da TUC sun yi zargin cewa, gwamnati na kokarin yin watsi da halin matsin da al’ummar ƙasar ke ciki a wanna lokaci, don haka ba za su zuba ido ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!