Labarai
A shirye nake na tsaya takarar gwamna a Kano – Muhyi Magaji
Tsohon shugaban hukumar karɓar ƙorafe-ƙorafe da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Barista Muhyi Magaji Rimin Gado ya ce a shirye yake ya tsaya takara a zaɓen 2023.
Muhyi Magaji ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Freedom Radio.
Ya ce, a shirye ya ke ya tsaya takarar gwamna a kakar zaɓen 2023 anan Kano.
“Lokacin da aka fara manna fasta ta a Kano da ke nuna alamun tsayawata takarar gwamna bana Kanon, da na dawo na tambaya sai aka shaida mun wasu ciyamomi ne suka yi hakan”.
“Da na bincika sai suka shaida mun cewa mutanen Kano irin mu suke so mu kawo musu sauyi, wannan ne ya sa na amsa tayin su da hannu biyu kuma na amince” in ji Muhyi.
Muhyi Magaji Rimin Gado ya ci gaba da cewa “An bar wa wasu mutane da basu cancanta ba sune suke mulkar jama’a, don haka za mu yi duk me yiwuwa mu amsa kiran al’umma don mu kawo sauyi”.
Wannan dai na zuwa ne watanni kaɗan bayan da gwamnatin Kano ta sauke Muhyi Magaji Rimin Gado daga shugabancin hukumar PCACC bisa zargin sa da almundanar kuɗaɗe.
You must be logged in to post a comment Login