Labarai
A tarihin siyasar Najeriya matsayina ya fi na Murtala koda ya kai mataimakin Gwamna – Doguwa

Shugaban masu rinjaye na majalisar tarayya Alasan Ado Doguwa ya ja kunnen mataimakin ɗan takarar Gwamnan APC a Kano Murtala Sule Garo.
Doguwa ya ce, shi bai jefi Murtala ba, bai kuma ji masa rauni ba.
“Amma ina so Murtala ya sani a tarihi da matsayi na a siyasar Najeriya a yanzu, matsayina ya fi nasa koda ya zama mataimakin Gwamna”.
Doguwa ya ce, har yanzu yana nan a mai biyayya ga jam’iyyar APC ta ƙasa.
A ranar Litinin ne dai rikicin jam’iyyar APCn Kanon ya sake fitowa fili bayan da aka rabu dutse a hannun riga a taron masu ruwa da tsakinta.
You must be logged in to post a comment Login