Labarai
A yau ake sa ran jirgin farko na maniyyatan Najeriya zai bar filin jirgin saman Abuja zuwa kasar Saudiya
A yau Asabar ake saran jirgin farko na maniyyatan kasar nan zai bar filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja domin zuwa kasar Saudiya.
Mai magana da yawun hukumar Fatima Usara ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a jiya Juma’a, ta ce; jirgin na kamfanin MAX Air zai kwashe maniyyatan jihar Kogi ne tare da wasu daga cikin jami’an hukumar jin dadin alhazai na jihar.
A cewar sanarwar jirgin wanda ake saran zai tashi da misalin karfe goma sha daya na safiyar nan zai kwashi maniyyatan ne zuwa birnin Madina.
Mai magana da yawun hukumar ta NAHCON ta cikin sanarwar dai ta kuma ce, har yanzu ana ci gaba rajistan bayanan maniyyata.