Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kungiyar NPO ta amince da sabon kudirin dokar aikin Jarida

Published

on

Kungiyar masu ruwa da tsaki kan harkokin yada labarai ta Kasa NPO tare da hadin gwiwar hukumar kula da gidajen Rediyo da Talabijin ta kasa BON sun nuna rashin amincewarsu da sabon kudurin dokar aikin Jarida, wanda suka ce ya saba da kundin tsarin mulkin kasa.

Kungiyar ta NPO dai ta kunshi kingiyar masu gidajen Jarida da kungiyar Editoci ta kasa da kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa NUJ wadanda suka gudanar da wata ganawa a tsakaninsu don fitar da wannan matsaya.

Yayin ganawar ta su sun gano cewa dokar za ta zamo karan tsaye ga ‘yancin fadar albarkacin baki da ‘yancin aikin Jarida tare da kare lafiyarsu, da kuma ‘yancin kafafen yada labarai a kasar nan.

Kungiyar ta NPO ta kara da cewa yanzu haka batun yana gaban Kotun Kolin kasar nan, kamar yadda wata sanarwa mai dauke da sa-hannun shugabanta Nduka Obaigbena ta bayyana, gami da sauran takwarorinsa da suka halarci taron.

Sauran wadanda suka sanya hannun su ne shugabar kungiyar Editoci ta kasa Funke Egbemode shugaban kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa NUJ Waheed Odusile da kuma shugaban masu gidajen Rediyo da Talabijin John Momoh.

Sannan kuma sun shawarci Majalisar Dattijai ta jingine batun har zuwa lokacin da Kotun Kolin kasar nan za ta hukunci kan makamancin batun da ke gabanta.

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!