Kiwon Lafiya
A yau shugaba Buhari zai jagoranci taron majalisar kasa a fadarsa dake Abuja
A yau Alhamis ne Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai jagoranci taron majalisar kasa a fadar sa dake Abuja.
Wannan dai shi ne karo na 3 tun bayan da shugaban kasar ya kama mulki a shekara ta 2015 yake jagorantar taron majalisar ta kasa, wanda ya hada da tsofafin shugaban kasa, a matsayin su na manbobin kungiyar.
Wadanda ake kyautatata zaton za su hallaci taron wanda aka tsara za’a yi a majalisar zartarwa ta kasa akwai tsofafin shugaban kasa Alhaji Shehu Shagari, da Olusegun Obasanjo da kuma tsohun shugaban kasa Goodluck Jonathan.
Sauran su ne tsohun shugaban kasa a mulkin soja janaral Yakubu Gowon mai ritaya da janaral Ibrahim Badamisi Babangida da Abdulsalami Abubakar mai ritaya da kuma shugaban kasa mai rikon kwarya Chief Ernest Shonekan.
Haka zalika mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo tare da shugaban majalisar Datijjai Bukola Saraki da na majalisar wakilai Yakubu Dokgara da babban mai shari’a ta kasa da gwamnonin jihohin 36 da kuma ministan shari’a kuma atoni Janaral Abubakar Malami dukkanin su a matsayin su na manbobin majalisar ta kasa.
Ana dai kyauta ta zaton cewa daga cikin abubawan da za’a tattauna akwai rikicin manoma da makiya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci taron farko a watan Okotoban shekara ta 2015 da kuma na biyu a watan Satumba shekara ta 2016.