Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

#EndSARS : Buhari na ganawa da tsofaffin shugabannin Najeriya

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari na tsaka da jagorantar ganawar gaggawa da tsofaffin shugabannin kasar nan  a fadar sa dake Abuja.

Wannan dai shi ne karon farko da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke ganawar ta kafar Internet da tsofaffin shugabanin kasar nan.

Wannan na kunshe ta cikin sanarwar da Mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan shafukan sada zumunta na Internet Bahair Ahmad ya wallafa a shafin sa na Twitter.

Daga cikin tsofafin shugaban kasar nan da shugaban kasa ke ganawa da su ta kafar Internet akwai Janaral Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo da Abdulsalami Abubakar da Goodluck Jonathan da kuma Earnest Shonekan

Ya yin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke tare da wasu daga cikin manyan kososhin gwamnati a fadar sa da suka hadar da, mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Oshinbajo da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha.

Sauran sune shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya Ibrahim Gambari da mai baiwa shugaban kasa shawara kan al’amuran tsaro mejo janaral Babagana Monguno mai ritaya da dai sauran su.

Ayyukan raya kasa : Buhari zai cigaba da shinfida tituna a Najeriya

Salon mulkin Buhari ya raba kan Najeriya – Obasanjo

Masu tada zaune tsaye nada boyayyiyar manufar da suke so su cimma – Buhari

Ana dai hasashen cewar, ganawar ba zai rasa nasaba da zangar-zangar lumana kan #EndSARS da ta rikide ta koma rikici shi ne zai mamaye abubuwan da zai mamaye ganawar ta Internet.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!