Labarai
A yi mana kyakykyawar fahimta akan ayyukan mu – KAROTA
Hukumar KAROTA ta ce, kamata ya yi ayi mata kyakykyawar fahimta akan ayyukanta na tsaftace harkokin sufuri a Tituna domin tana yi ne don sauya dabi’ar masu karya doka, amma bata nufin cin zarafin kowa.
Shugaban Hukumar Baffa Babba Dan’agundi ne ya bayyana haka a taron karramashi da gamayyar kungiyoyin sufuri na Kano KTP suka yi saboda gudunmawar da KAROTA take baiwa harkar Sufuri a Kano.
Baffa Babba yace KAROTA ba ta gunar da kowane aiki don musgunawa wasu ko don ta ci zarafin wasu mutane sai dai yawan kokawa da masu ababen hawa ke yi da ita suna yi ne saboda basa san gaskiya da kuma bin doka.
A jawabin sa shugaban gamayyar Kungiyoyin Sufuri na Kano KTP Ashiru Umar cewa yayi daga lokacin da Baffan ya karbi KAROTA ya sauya mata alkibla musamman wajen tsaftace harkar zirga zirga a titunan Kano baki daya.
Shi kuwa shugaban Hadaddiyar kungiyar Direbobin Tifa ta kasa reshen jihar Kano Mamuni Ibrahim Takai yabawa Baffan ya yi musamman wajen sauya fasalin yadda mutane suke tuka ababen hawansu a baya wajen saba dokokin tuki batare da suna bin doka da Oda ba.
Wakilin mu Abdulkarim Muhd Tukuntawa ya ruwaito gamayyar Kungiyoyin na Sufuri KTP sun baiwa shugaban Karota Baffa Babba Dan Agundi lambar girmamawa guda biyu saboda kokarinsa na tsaftace harkar zirga zirga a fadin jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login