Connect with us

Labarai

Yanzu-yanzu: An ceto matashin da ya rataye kansa a Kano

Published

on

Rahotanni daga unguwar Ƴan Kaba da ke nan Kano na cewa an samu wani matashi ya rataye kansa a jikin bishiya

Matashin ɗan shekaru 29 mai suna Mukhtar Umar ya rataye kan nasa ne a daren ranar Asabar.

Daga bisani ne kuma al’umma suka farga, suka sanar da jami’an tsaro, inda baturen ƴan sanda na Bompai SP. Aliyu Musa ya jagoranci ƴan sanda domin ceto shi.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya shaida wa Freedom Radio cewa, ƴan sanda sun ceto matashin cikin ƙoshin lafiya.

Sai dai a cewar sa, ƴan uwan matashin sun shaida musu cewa ya taɓa samun larurar ƙwaƙwalwa saboda ta’ammali da miyagun ƙwayoyi.

DSP. Kiyawa ya ce, yanzu haka sun shiga faɗaɗa bincike kan matashin domin ɗaukar matakin da ya dace.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Subscribe to Freedom Radio via Email

Enter your email address to subscribe to this site and receive notifications of new posts by email.

Join 338,433 other subscribers.

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!