Connect with us

Labarai

Abduljabbar na fama da rashin lafiya a gidan gyaran hali

Published

on

Lauyan Malam Abduljabbar Kabara Barista Rabiu Shu’aibu Abdullahi ya tabbatar da cewa malamin bashi da lafiya yanzu haka da yake tsare a gidan gyaran hali.

Sai dai Barista Rabiu ya musanta zargin da ake yaɗawa cewar an sakawa malamin guba a abinci a gidan gyaran halin da yake tsare.

“tabbas Malam bashi da lafiya, amma tuni an samo likita ya duba shi kuma ya bashi magani, har ma ya samu sauki a halin yanzu” Lauyan Abduljabbar.

Itama hukumar kula da gidan gyaran hali na Kano DSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa ya ce, malamin bai taba shan ruwa ko abincin gidan gyaran hali ba, a don haka babu wani abu da ya same shi.

“Mun samu labarin wani lauya ne ya fitar da labarin cewa an ba shi guba a inda ya ke tsare, wannan ne ya sanya muka baza jami’an mu don gano wanda yayi wannan kalami tare da ɗaukar mataki a kan sa” inji DSC Musbahu Lawan Kofar Nasarawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!