Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Janar Abdulsalami Abubakar ya bukaci bata-gari da masu garkuwa da mutane da su tuba

Published

on

Tsohon Shugaban Kasa, Janar Abdulsalami Abubakar ya bukaci bata-gari da masu garkuwa da mutane dasu tuba domin baiwa al’umma damar cigaba da gudanar da ayyukan su cikin kwanciyar hankali.

Janar Abdulsalami Abubukar ya bayyana hakan lokacin da yake taya al’ummar Musulmai murnar zagayowar Sallah babba a Minna babban birnin jihar Naija.

Abdulsalami Abubukar yace ayyukan batagari a fadin kasar nan na jawo koma baya a al’amura da dama, a don haka yake shawartarsu da su bar al’ummar Najeriya su zauna lafiya tare da gudanar da bukuwan Sallah kamar yanda aka saba.

Janar Abdulsalami Abubakar yayi fatan al’ummar Najeriya za suyi bukukuwan Sallah lafiya su gama lafiya ba tare da samun tashin hankali ko wani fargaba ba daga hannun bata garin ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!