Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Addini

Abin da ya sa bama kama ƴaƴan masu galihu – Hisbah

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta yi ƙarin bayani kan zargin da ake mata na bada fifiko kan hukunta marasa ƙarfi.

Hakan dai ya biyo bayan ƙorafe-ƙorafen da wasu suka riƙa yi musamman a kafafen sada zumunta.

Jama’a da dama sun zargi hukumar da kau da kai daga abin da masu mulki da masu kuɗi ke yi.

Kan hakan ne Freedom Radio ta tuntuɓi Babban Daraktan hukumar Dr. Aliyu Musa Aliyu Kibiya.

Hisbah ta kori babban jami’inta da aka samu da matar aure a Otal

Mun karbi korafe-korafe fiye da kowanne lokaci daga farkon shekara nan – Hisbah

Dr. Aliyu Kibiya ya ce, Hisbah tana yin da’awa ga kowa da kowa, sai dai a bisa mataki-mataki.

Saboda haka, irin salon da ake yiwa gama-garin mutane, ba shi ne wanda za a yiwa manyan mutane ba.

Ya ci gaba da cewa “Mu yadda mu ke yiwa kallon abin, in aka ce shugaba ya yi laifi ba tarbiyyar musulunci ba ce, a je masallaci ana faɗa a lasifiƙa”.

“Akwai waɗanda suna da hanyar da za su samu shugaba su da shi, kuma dama aikin shi ne isar da saƙo, shi kuma Allah shi yake shiryarwa”.

Dr. Kibiya ya ƙarara nanata cewa, “Akwai irin da’awar da za a yiwa normal mutane (gama-gari), akwai kuma da’awar da za a yiwa shugabanni”.

Freedom Radio ta sake miƙa wannan tambaya ga Babban Kwamandan hukumar ta Hisbah Malam Muhammad Haruna Ibn Sina.

Ya ce, hukumar ta kama da yawa daga ƴaƴan masu kuɗi, kuma suna kan kamawa a kowane lokaci.

“Mun kama ƴaƴan masu kuɗi da yawa, kuma muna kamowa a koda yaushe”.

Masu amfani da kafafen sada zumunta dai sun sha sukar hukumar kan yadda ta kauda kai game da bukukuwan ƴaƴan shugabanni.

Amma kuma tana kame ƴaƴan talakawa da laifin shigar banza ko cakuɗuwa.

Ko kun san ina aka kwana game da sabinta dokar hukumar Hisbah?

Shin ayyukan Hisbah na yanzu sun dace da abin da dokar da ta kafata ta gindaya?

Zamu ɗora a gaba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!