Labarai
Abin da ya sa majalisa ta buƙaci a cire shugaban hukumar tattara haraji
Majalisar dokokin jihar Kano ta buƙaci gwamnatin jihar Kano ta kori shugaban hukumar tattara kuɗaɗen haraji ta jihar Kano Abdurrazak Datti Salihi.
Majalisar ta cimma matsayar ne a zamanta na Talata bayan da shugaban hukumar ya gurfana a gabanta kamar yadda ta bukata.
Tun da fari majalisar ta bukaci da ya yi mata bayani kan wata takarda da ya ce shi da kansa ya aikewa hukumar ƙasa da safiyo kan umarnin ta hana ma’aikatanta bai wa kwamitocin majalisar kowacce irin takarda ko bayani kan harkokin haraji.
Sai dai Abdurrazak Datti Salihi ya ce, ba haka abin yake ba, anan ne shugaban majalisar Injiniya Hamisu Ibrahim Chidari ya sanya aka ba shi kundin tsarin mulkin ƙasa tare da sanya shi ya karanta sashe na 128 da na 129.
Sashin dai su ne ya bai wa majalisar ikon yin sammacen kowanne mutum a duk inda yake don ya bada bayanai.
Sai dai bayan kammala zaman sirri da majalisar ta yi ne mambobinta suka amince da ɗauka matakin sauke shi cikin sa’o’i 48 sakamakon kin yin amfani da dokar kundin tsarin mulkin.
Da yake ganawa da manema labarai bayan kammala zaman majalisar, shugaban masu rinjae na majalisar Alhaji Labaran Abdul Madari, ya ce, laifin da ya aikata ya saɓa da dokar ƙasa har ma da kundin tafikar da majalisar.
You must be logged in to post a comment Login