Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Abin da ya sa muka raba gari da mai horaswarmu – Kano Pillars

Published

on

Ƙungiyar ta Kano Pillars ta ce, rashin shaidar ƙwarewa ta hukumar ƙwallon ƙafa ta Africa ce, ta sanya ta raba gari da maihorarwarta.

Shugaban hukumar gudanarwar ƙungiyar, Alhaji Surajo Shu’aibo Yahaya Jambul ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai a ranar Lahadi.

Jambul ya ce, a yanzu ƙungiyar bata da mai horaswa, domin babu wanda ke riƙe da lasisin kwarewa daga hukumar kwallon  ƙafa ta Afrika wato CAF, ya kuma godewa tsohon mai horaswar ƙungiyar ta Kano Pillars tare da yi masa fatan alkhairi.

Sai dai a nasa ɓangaren, tsohon mai horarwarta Ibrahim Musu Jugunu ya shaidawa Freedom Radio cewa, har yanzu yana nan a muƙamin shi.

A ranar Asabar ne, ƙungiyar ta sanar da cewa, dama ta samu ga duk mai sha’awar gurbin maihorarwarta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!