Labarai
Abin da ya sanya Buhari ya dakatar da Hadiza Bala Usman
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya dakatar da shugabar hukumar kula da tashoshin Jiragen Ruwa ta ƙasa (NPA) Hajiya Hadiza Bala-Usman.
Hakan na cikin wata sanarwa da mataimaki na musamman ga shugaban ƙasar kan yaɗa labarai Malam Garba Shehu ya fitar cikin daren Alhamis ta shafin sa na Twitter.
Sanarwar ta ce, an naɗa babban Daraktan Kuɗi da Gudanarwa na hukumar, Mohammed Bello-Koko a matsayin Muƙaddashin Daraktan hukumar.
Rahotonnin da jaridar The Nation ta rawaito daga ma’aikatar ga Sufuri, sun nuna akwai rashin jituwa a ƴan kwanakin nan tsakanin ministan sufuri, Rotimi Amaechi da kuma Hadiza Bala Usman.
Majiyar jaridar ta kuma ce, a ranar Juma’a ministan Sufurin Rotimi Amechi zai yi ƙarin bayani dangane da dakatarwar da aka yiwa shugabar hukumar.
A kwanakin baya ne dai shugaban ƙasa Muhammad Buhari ya amince Hadiza Bala Usman ta ci gaba da gudanar da shugabancin hukumar a karo na biyu.
An naɗa Hadiza Bala a shugabancin hukumar tun shekarar 2016 bayan da aka sauke Habib Abdullahi daga muƙamin.
You must be logged in to post a comment Login