Addini
Abin da ya sanya Kabiru Gombe zai maka Ɗan Sarauniya a Kotu
Sakataren ƙungiyar Izala na ƙasa Malam Kabiru Haruna Gombe ya yi barazanar maka tsohon Kwamishinan ayyuka na Kano Engr. Mu’azu Magaji Ɗansarauniya a gaban kotu.
Kabiru Gombe ya bai wa Ɗansarauniyar awanni 12 domin ya fito ya nemi afuwa, kan labarin da ya wallafa game da shi a ranar Alhamsi.
A wani saƙo da ya fitar a shafinsa na Facebook, Mu’azu Magaji ya bayyana cewa an samu wata waya da Kabiru Gombe ya ke gindayawa Shugaban APC na ƙasa Mai Mala Buni sharaɗi.
Sharuɗin shi ne za su fice daga jam’iyya matuƙar aka shigo da tsohon Gwamnan Kano Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso cikin ta.
Sai dai a martaninsa, Kabiru Gombe ya wallafa a Facebook cewa, shi bai taɓa waya da Mai Mala Buni ba.
Ya ci gaba da cewa “Wannan ƙarya da ka kantara min mai haɗe da cin mutunci mafi ƙololuwa a rayuwa, sam ba a yita ba, bamu da alaƙa da duk wani mai mulki da ya wuce ta addini”.
Malamin ya ƙara da cewa tuni ya fara magana da lauyoyinsa, domin garzayawa kotu matuƙar Mu’azu Magaji bai fito ya janye maganarsa ba tare da neman afuwa.
Ɗan Sarauniya ya nemi afuwa.
Sai dai jim kaɗan bayan wannan saƙo na Kabiru Gombe, tuni Mu’azu Magaji ya sake fitowa ya nemi afuwa, inda ya ce yana roƙon Malam da ɗalibansa su yafe masa.
Ɗan Sarauniya ya ce, shi ma a wani shafi ya gani, kuskurensa kawai sh ne, rashin bayyana inda ya samo labarin a shafinsa, don haka mutane suka ɗauka shi ne ya ƙirƙira.
Mutane na ci gaba da tsokaci a kai:
Yanzu haka dai tuni masu amfani da kafafen sada zumunta suka shiga bayyana ra’ayoyi kan wannan batu, waje guda kuma Malam Kabiru Gombe bai sake cewa komai ba, yayin da shi kuma Ɗan Sarauniya ya cike shafinsa da jerin gwanon saƙonnin neman afuwa.
You must be logged in to post a comment Login