Connect with us

Labarai

Abinda da ake yadawa a kaina kan makomata a siyasa karya ne- Kwankwaso

Published

on

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi watsi da rahotanni da ke alaƙanta cewa yana daf da komawa wata jam’iyya, da kuma batun cewa zai shiga haɗaka da wasu jam’iyyu, lamarin da ya ce ƙanzon kurege ne kawai domin ba da yawunsa ba.

Wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, Kwankwaso ya ce raɗe-raɗin baida tushe balle makama kuma labaran ƙarya ne kawai na siyasa.

Ya ce, ya daina yin tsokaci kan lamuran siyasa da ke faruwa a Najeriya, kuma zai ci gaba da yin haka har zuwa wani lokaci.

Don haka ne, ya buƙaci al’umma da su amince da sakonni da suka fito daga shafukansa da kuma majiyoyi da aka yarda da sahihancinsu ba daga wasu wurare na daban ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!