Rahotonni
Abinda ke ciwa mutane tuwo a kwarya a asibitin AKTH Kano
Latsa hoton dake sama domin sauraron cikakken bayanin cikin sauti.
Wani bincike da Freedom Radio ta yi ya gano yadda ake fama da matsala wajen tsarin karbar kudi a zamanance da ake kira da “Cashless Policy” a asibitin koyarwa na Aminu Kano.
Wato dai babu kyakkyawan tsari na zamani wajen biyan kudi daga masu mu’amala da asibitin ta tsarin POS.
A wannan zamani da muke ciki na takaita ta’ammali da kudade a hannun jama’a wato “Cashless Policy,” ana ganin hakan ba karamin koma baya bane ga asibitin koyarwa kamar na Aminu Kano.
Labarai masu alaka:
Kano: Masu fama da cutar koda sun roki gwamnati ta mayar da wankin Koda kyauta
Asibitin AKTH zai gudanar da jarabawar kwarewa ga likitoci fiye da dubu
A yanzu dai babu damar biyan kudi ta hanyar amfani da zamani a asibitin sai dai abi tsarin karbar zunzurutun kudi tsaba ta hannu-hannu.
Wannan tsari dai ya haifar da cunkuso a wurin biyan kudin domin kuwa sai mutum yabi dogon layi kafin ya samu biyan kudin aiki a asibiti.
Wakilin Freedom Radio Nasir Salisu Zango ya gano yadda hatta masu sayar da abinci a asibitin Malam Aminu Kano na amfani da na’urar hada-hadar kudi ta POS.
Koda yake Freedom Radio ta gano cewa akwai wanda ya kafa sana’ar cirar kudi ta na’urar POS din a harabar asibitin, amma hakan ya gagara samuwa a tsarin ta’ammali da hada-hadar kudi a asibitin na Aminu Kano.
Da wannan ne Freedom Radio ke shawartar hukumar asibitin kan tayi duba, don tausayawa al’ummar dake hulda da asibitin.
Labarai masu alaka:
Asibitin kashi na Dala ya fadakar da dalibai illar gobara
AKTH ya samu nasarar gudanar da aikin kwakwalwa karo na biyu