Connect with us

Labarai

Kano: Masu fama da cutar koda sun roki gwamnati ta mayar da wankin Koda kyauta

Published

on

Masu fama da cutar Koda a jihar Kano sun roki gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje kan ya mayar da yin aikin wankin koda kyauta a jihar.

Jihar Kano dai ita ce jihar da ta kere sauran jihohi yawan masu fama da cutar koda a Najeriya, a don haka masu fama da larurar suka garzayo shirin Inda Ranka na nan Freedom Radio, inda suka nemi gwamnatin jihar tayi duba na tsanake domin kulawa da lafiyar su.

A cewar su tuni Gwamnan jihar Borno Farfesa Baba Gana Zulum ya mayar da aikin wankin kodar kyauta a jihar sa, a don haka jihar Kano ita tafi can-canta da tayi wannan aiki.

A karshe masu cutar sun bayyana yadda suke kashe kudade a kowane lokaci don wannan jiyyar.

Labarai masu alaka:

Gwamnatin Kano za ta fara karrama ma’aikatan lafiya

Abubuwan da ya kamata ku sani gami da lafiyar Idanu

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!