Labarai
Abinda talakawa ke so za mu yi a kasafin 2026- Gwamnatin Katsina

Gwamnatin jihar Katsina ta ce, za ta yi amfani da abin da al’ummar ta ke son a yi musu ne a kasafin kudin shekarar 2026 da ke tafe.
Hakan na zuwa ne yayin wani taron jin ra’ayin jama’a kan kasafin kudin data gudanar a mazabunta 361.
Da ya ke jawabi yayin rufe taron jin ra’ayin mutanen a karamar hukumar Kankara, mataimakin gwamnan jihar Alhaji Faruk Lawan Jobe ya tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta cigaba da fifita bukatun al’ummarta.
You must be logged in to post a comment Login