Labarai
Yadda aka hada Kudanci da Arewacin kasar nan kafin samun ‘yan cin kai
A shekarar 1914 ne karkashin Jagorancin Gwamna Janar Fredrick Lugard ne aka hade yankunan arewa da kudu, karkashin kasa daya dunkulalliya, wadda aka sanyawa suna Nigeria.
Turawan mulkin mallaka sun ci gaba da mulkin kasar inda a yankin kudu, suke mulki kai tsaye yayin da a yankin arewaci kuma suka gudanar da mulki ta hannun masarautun gargajiya.
Bayan an yi ta kai kawo a kan lokacin da ya dace a mika mulki, a karshe an amince da baiwa Nigeria’r ‘yan cin kanta ranar daya ga watan Octoba na shekarar 1960.
Wadanda suka ganewa idanunsu yadda aka gudanar da mulkin mallaka gabanin samun ‘yancin kan na bayyana cewar lamarin babu kyawun gani.
Ra’ayoyi dai sun bambamta akan halin da Najeriyar ke ciki, bayan cika shekaru hamsin da tara da samun ‘yancin mulkin kai.
Yayin da wasu ke cewar kasar ta samu ci gaba, wasu kuwa, suna cewa ba su ga wani cigaba da kasar ta samu ba a tsawon wannan lokaci.
Najeriya ta samu ‘yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoban shekara ta 1960. Tun kafin ranar an yi ta yin bukukuwa daban daban domin nuna murna.
Gimbiya Alexandra tana karanta sakon Sarauniyar Elizabeth ta Ingila, a jawabin da aka gabatar a dakin taro na Royal Pavilion dake Legas ranar da aka baiwa Najeriya ‘yancin kai, wato 1 ga Oktoban 1960. Inda Fira Minista Sir Abubakar Tafawa Balewa yake zaune a damanta.
Wannan jawabi da Gimbiyar ta karanta a madadin Sarauniya, wani muhimmin mataki ne a bikin da aka gudanar na baiwa Najeriya ‘yancin kanta daga hannun Turawan mulkin mallaka na Ingila, an dai gudanar da taron ne a Legas.
Sabon Fira Ministan Najeriya Alhaji Sir Abubakar Tafewa Balewa a hagu, Gimbiya Alexandra a tsakiya, Gwamna Janar James Robertson lokacin bikin baiwa Najeriya ‘yancin kai.
Gimbiya Alexandra na zaune a tsakiya, inda take wakiltar Sarauniya Elizabeth II, a dakin taro bada ‘yanci a Legas, ranar 3 ga watan Oktoban 1960, inda ta bude ginin zauren majalisun dokokin Najeriyar. A tare da ita akwai Gwamna Janar Sir James Robertson tare da matarsa Lady Robertson.
Daga hannun dama akwai cif Obafemi Awolowo; Firimiyan Yamma; Alan Lennox Boyd Sakataren Turawan mulkin mallaka, Sir Ahmadu Bello, Firimiyan Arewa; Sir James Robertson Gwamnan tarayyar Najeriya da kuma Dr Nnamdi Azikiwe,Firimiyan Gabas, a wajen taron kundin tsarin mulki da aka gudanar a birnin London.
Sabon Fira Ministan Najeriya Alhaji Sir Abubakar Tafewa Balewa, na biyu daga dama, tare da shi akwai Gimbiya Alexandra lokacin bikin baiwa kasar ‘yanci daga Turawan Ingila a ranar 1 ga watan Oktoba na shekarar 1960.
Menene ra’ayoyin ku kan irin cigaban da kasar nan ta samu kawo yanzu