Labarai
Abinda ya sa ban ce komai ba kan batun sanya Hijab a Jamia: Sarkin Musulmi
Sarkin musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya bayyana cewa Musulmi a fadin Najeriya , da ma Duniya baki daya na fuskantar babban kalubalen da ka iya riskarsu nan ba da jimawa ba.
Ya bayyana haka ne a yayin da ake gudanar da babban taron kungiyoyin Musulmi na yankin kudu maso yammancin kasar nan MUSWEN wanda aka gudanar a dakin taron da ke masallacin jami’ar Ibadan babban birnin jahar Oyo.
Sarkin musulmin wanda shine shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci ta kasa NSCIA ya bukaci daukacin al’ummar Musulmi da su kasance masu hadin kai da son juna.
Ya kara da cewa akwai rade-radin da ke zagayawa kafafan sada zumunta Soshiyal Media da ke cewa har kawo yanzu sarkin Musulmi bai ce komai ba dangane da matsalar sanya hijabi da ke kai kawo a jamiar ta Ibadan, kasancewarsa shugaban jami’ar.
Ya kara da cewa ya kamata jama’a su san cewar Musulunci , Addini ne da ke umartar mabiyansa da su kasance masu bin doka tare da kauracewa daukar matakai da kansu, da tabbatar da cigaban kasa.
Sarkin Musulmin ya ce ba zai yiwu a yanzu da zancen ke gaban kotu ba ,zai iya tofa albarkacin bakinsa har sai kotu ta yanke hukunci tare da kira da kungiyoyin musulmi da su karfafawa sanya hijabi domin cigaban Musulunci.
Ya kara da cewa kan Musulmai a rarrabe yake, lokaci yayi da za’a hada kan Musulmi,tare da kauracewar hada siyasa da addini, domin mayar da wasu batutuwa a matsayin wani abu na siyasa baya haifar da da Da mai ido.
Ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su kasance masu daukar nauyin karatu tare da samar da ayyukan yi a fadin kasar.
Da yake jawabi sakataren kungiyar Farfesa Dawud Ujobi ya bukaci Musulmi da su daina dangantaka Addini da siyasa.