Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin musulmi ya nemi gwamnati ta kawo karshen matsalar tsaro

Published

on

Sarkin Musulmi

Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ya bukaci gwamnatin tarayya da ta bai wa bangaren tsaro fifikon da ya dace da , don kawo karshen zubar da jinin al’umma babu gaira babu dalili a fadin kasar nan.

Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na uku ya bayyana hakan ne a wajen wani taro kan harkokin tsaro mai taken: ‘Umaru Shinkafi Security and Intelligence Summit’ wanda ya gudana a garin Sokoto.

A cikin wata sanarwar bayan taro mai dauke da sa hannun daya daga cikin ‘yan kwamitin shirya taron, Mahmud Jega, ta ruwaito Sarkin na musulmi na bayyana damuwarsa kan yadda kashe-kashen jama’a ke ci gaba da faruwa a kasar nan.

Mahalarta taron dai sun gabatar da mukalu tare da shawartar gwamnatoci a dukkan matakai da su bullo da sabbin dabaru na dakile matsalolin tsaro da ke addabar kasar nan.

Haka zalika ta cikin takardar bayan taron, Sarkin na musulmi ya kuma bukaci gwamnatin tarayya da rundunar sojin kasar nan da su kara karfafa rundunar shiyya ta takwas da ke Sokoto da sauran shiyoyi na sojoji da ke yankin arewa maso yammacin kasar nan don kawo karshen matsalar ayyukan ‘yan bindiga.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!