Connect with us

Labarai

Wata matashiya ta yi yunkurin kashe kanta sakamokon auren dan shekaru 70

Published

on

Lamarin dai ya faru ne a ranar juma’a 15 ga wannan wata da muke ciki na Nuwamba, inda matashiyar ta yi yunkurin shiga cikin na’urar bada hasken lantarki watau Transformer ,a unguwar Sharada dake yankin karamar hukumar birnin Kano a makon da ya gabata, bayan da ta yo tattaki tun daga unguwar Rimin Kebe da ke yankin karamar hukumar Ungogo.

Wani daga cikin mutanen da suka kai mata dauki ya bayyana cewa matashiyar ta zo wurin su ne inda take shaida musu cewar, an yi mata aure ne da wani tsoho wanda bata son shi don haka ne take neman mafita.

Haka kuma ta kara da cewa, tana gama fada musu hakan ne sai kawai suka ga ta nufi dakin injin wutar inda ta yi yunkurin kashe kanta, sai dai sun yi gaggawar hana ta shiga.

A tattaunawar Freedom Radio da dan uwan matashiyar mai suna Malam Muhammad Rimin Kebe, ya bayyana cewa, kimanin shekaru biyu Kenan da daura auren ta da dattijon amma ba da son ranta ba.

Kan haka ne kungiyar kare hakkin dan Adam ta shiga lamarin inda shugaban kungiyar Karibu Lawan Kabara ya bayyna cewa, za su yi iya yinsu wajen ganin sun kwato wa matashiyar hakkinta.

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!