Labarai
Abinda yasa ban barwa Oshinbajo jan ragamar kasa ba -Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya zayyano dalilan da suka sanya bai barwa mataimakin sa ya ja ragamar shugabancin kasar nan ba, idan yayi tafiya zuwa kasashen waje.
Muhammadu Buhari yace kundin tsarin mulkin kasar nan bai tanadi lalle sai shugaban kasa ya baiwa mataimakin sa jan ragamar kasar nan ba.
Haka zalika shugaban kasar yayi ikirarin cewar, kundin tsarin mulkin kasar nan ya bayyana cewar sai dai in har shugaban kasa zai kai kwanaki 21 a wajen kasar nan shi ne ya zama tilas ya mika wa mataimakin sa ragamar jagorancin kasar.
A cewar Muhammadu Buhari kundin tsarin mulkin shekara ta 1999 da aka yi wa garanbawul ya lissafo ayyukan shugaban kasar Najeriya yayin da kuma in da zai tafi hutu sai ya mika ragamar mulkin kasar nan ga mataimakin shugaban kasa.
Sai da wasu na zargin cewa dangantaka ta yi tsami tsakanin shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakin sa farfesa Yemin Osinbajo, ya sanya ake jin kan su a yanzu.
Rahotannin sun bayyana cewar tun bayan da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da kwamitin bada shawarwari kan tattalin arzikin kasa wasu ke ganin cewar an kwacewa mataimakin shugaban kasa aikin sa bayan da yake jagorantar majalisar tattalin arzikin kasa.
Har ila yau, a kwanakin baya ne, shugaban kasa ya kori shugaban kwamitin kwato kadarorin gwamnati Okon Obono-Obla wanda mataimakin shugaban kasa ke kula da ofishin sa.