Labarai
Abinda ya sa Ganduje ya haramta yin goyo a babur
Gwamnatin jihar Kano ta haramta yin goyan biyu ko fiye da haka a babura masu kafa biyu a jihar nan.
Shugaban hukumar karota Baffa Babba Dan’Agundi ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labarai a yammacin yau.
Baffa Babba Dan’Agundi, ya kara da cewa hukumar KAROTA ta lura cewa wasu na neman dawo da sana’ar a caba a jihar nan a dan haka yazama wajibi a dauki wannan mataki na haramta yin goyo a babura masu kafa biyu.
Ya kuma ce hukumar karota zata fara kama duk wanda ya karya dokar yin goye a babur mai kafa biyu daga gobe alhamis sha takwas ga watan da muke ciki kuma hukumar bazata saurarawa duk wanda yakiyin biyayya ga dokar ba.
Baffa Babba Dan’Agundi ya kuma yi kira ga masu ababen hawa dasu runka sanya takunkumin rufe hanci da baki dan kaucewa kamuwa da cutar Covid-19.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa, ya rawaito cewa hukumar KAROTA na kira ga al’umma dasu cigaba da bawa hukumar hadin kai ta hanyar bin dokokin kan titi.
You must be logged in to post a comment Login