Labaran Kano
Abinda yasa kungiyar JOHESU ke son tsunduma yajin aiki
Gamayyar kungiyar ma’aikatan lafiya ta kasa JOHESU ta yi barazanar tafiya yajin aikin sai baba ta gani matukar gwamnatin tarayya ta gaza biya musu bukatun su.
Shugaban kungiyar ta kasa Biobolemoye Joy Josiah ne ya bayyana hakan ta bakin Sakataran gamayyar kungiyoyin ma’aikatan lafiya na kasa reshen jihar Kano, Kwamared Auwalu Yusuf Kiyawa yayin ziyarar da suka kawowa membobin su dake Asibitin kashi na Dala dana Aminu Kano.
Kwamared Auwalu Yusuf Kiyawa ya kuma ce ma’aikatan lafiya a kasar nan basa samun Karin girma da wuri tare da rashin kula da walwalar su da gwamnatin tarayya batayi da kuma rike musu albashin su na watanni biyu da gwamnati tai.
Da yake bayani game da ziyarar da gamayyar kungiyoyin na JOHESU suka kawo masa shugaban Asibitin kashi na Dala Dakta Muhammad Nuhu Salihu cewa yayi hukumar asibitin zatai iya kokarinta wajen ganin ta mika korafin su zuwa ga ma’aikatar lafiya ta kasa.
Wakilin mu Abubakar Tijjani Rabi’u ya rawaito cewa shugaban Asibitin na Dala ya ce ya kamata gwamnati ta kara yawan kudaden da take kashewa a bangaren lafiya kamar yadda ake kashe kudade masu yawa a fannin tsaro.