Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Abokin Kowa: Sabon Kwamishinan ƴan sandan Kano ya kama aiki

Published

on

Sabon Kwamishinan ƴan sandan Kano Sama’ila Shu’aibu Dikko ya kama aiki yau Jumu’a.

An haifi Sama’ila Dikko a ranar 27 ga watan Yuli na shekara 1962 a garin Lere na jihar Kaduna.

Bayan ya kammala Firamare da Sakandire daga shekarar 1970 zuwa 1982 ya shiga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya inda ya yi digirinsa a kan nazarin ayyuka.

Bayan ya kammala ya yi bautar ƙasa a jihar Rivers a 1986 zuwa 1987.

Daga nan kuma sai ya shiga aikin ɗan sanda a ranar 3 ga watan Maris na shekarar 1990.

Sabon Kwamishinan ‘Yan sandan Kano Sama’ila Shu’aibu Dikko

Dikko ya samu horo a kwalejin ƴan sanda da ke Kaduna.

Ya riƙe muƙamai da dama a rundunar ciki har da dogarin tsaron mataimakin Gwamnan jihar Nassarawa.

Kafin naɗin sa a wannan matsayi shi ne mataimakin Kwamishinan ƴan sanda na jihar Adamawa.

Hotunan yadda Kwamishinan ya shiga ofishinsa da ke Shalkwatar ‘Yan sanda ta Bompai

Mun tattaro waɗannan bayanan ne daga shafin mai magana da yawun ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa na Facebook.

KANO STATE POLICE COMMAND DIARY 19/02/2021

TODAY, 19/02/2021 CP SAMA’ILA SHUAIBU DIKKO, fsi…

Posted by Abdullahi Haruna Kiyawa on Friday, February 19, 2021

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!