Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Yadda aka sami asarar rayuka a hatsarin mota a Kano

Published

on

Ana fargabar mutane biyu sun rasa rayukansu sanadiyar wani mumman hatsarin mota da ya abku da ranar yau akan titin western bye pass da ke nan birnin Kano.

Shaidun gani da ido sun ce hatsarin ya faru ne lokacin da wani babur din adaidaita sahu ya kaucewa fadawa rami wanda sanadiyar haka ya kora wasu matasa biyu da ke kan babur kirar Jincheng suka fado gaban wata motar dakon kaya wadda ta takesu.

Wasu daga cikin wadanda lamarin ya faru akan idanunsu, sun shaidawa freedom radio cewa, motar dakon kayan, tabi ta kan matasan ne bayan da suka fadi daga kan babur din.

Wakilin mu Umar Idris ya ruwaito cewa, tuni ‘yan sandan suka dauki matasan zuwa asibiti.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!