Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Nishadi

Abubuwan 6 da Sarkin Waƙa murabus ya ce bayan fitowarsa daga gidan gyaran hali

Published

on

Hoton Naziru M. Ahmad kenan jim kadan bayan fitowarsa daga gidan gyaran hali.

A makon da ya gabata ne aka sako Naziru Sarkin Waƙa bayan da ya cika sharuɗan belin da kotu ta sanya masa.

Hukumar tace finafinai ta Kano ce ke tuhumar Nazirun da fitar da wasu waƙoƙi ba bisa ƙa’ida ba.

Freedom Radio ta zanta da Nazirun jim kaɗan bayan fitowarsa daga gidan gyaran halin.

Ga jerin wasu abubuwa 6 da ya faɗa a zantawar.

Abu na farko da ya ce, bai aikata laifin da ake zarginsa ba.

A cewar sa, waƙoƙin sun jima da fita kuma ba shi ne yayi dillancin fitar da su ba.

Na biyu ya ce, bai taɓa ƙullatar wani cikin abokansa a harkar waƙa ba.

Na uku, Nazirun ya ce, shi ba ɗan masana’antar Kannywood ba ne, kawai dai zumunci ne a tsakaninsu, kuma bai taɓa yin rijista da su ba.

Labarai masu alaka:

Kotu ta saki Naziru Sarkin waka

Naziru ya yi Murabus daga Sarkin Wakar Sarkin Kano

Na huɗu ya ce, ya ga abubuwan mamaki dana nishaɗi a gidan yarin.

Ya ƙara da cewa, mafi yawan da ya gani matasa ne, haka kuma ya je kallon ƙwallon ƙafa a gidan.

Sannan ya haɗu da jama’a da dama a gidan waɗanda suka nuna masa soyayya.

Na biyar ya ce, ba ƙaramar wahala ya ke sha ba, a lokacin da ya ke haɗa waƙa hakan yasa waƙoƙinsa su ke zama fitattu.

Nazirun ya ce, ya kan shafe sama da wata guda ba tare da ya je ko ina ba don samar da waƙa.

Abu na shida, Nazirun yayi alƙawarin zai fitar da wata sabuwar waƙa da zata yi bayani kan rayuwarsa a gidan gyaran hali.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!