Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kotu ta saki Naziru Sarkin waka

Published

on

Kotun Majistre da ke No-man’s-land a jihar Kanon Najeriya, ta saki fitacce mawakin nan Naziru Sarkin Waka, bayan ya shafe kwanaki biyu a tsare.

Lauyan mawakin, Barista Sadik Sabo Kurawa, ya shaidawa Freedom radio cewa, wanda ake tuhumar be aikata laifin da ake zarginsa ba.

Kotun dai na tuhumar mawakin ne, bisa zargin sakin wasu wakoki ba tare da sahalewar hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ba.

Rahotanni sun tabbatar da cewa Alkalin kotun, mai shari’a Aminu Gabari, ya sake shi ne, bayan ya cika sharuddan da aka gindaya masa.

Daga cikin sharuddan da mawakin aka bukaci ya gabatarwa kotun akwai;

Zai gabatar da mutane biyu da za su tsaya masa, kuma dole daya ya kasance mahaifinsa ko dan ‘uwansa, dayan kuma ya kasance wakilin Gabas, Arewa ko kuma Kudu a Kano, ko kuma daya daga cikin kwamandojin Hisbah a kananan hukumomin jihar 44.

Haka zalika zai ajiye kudi naira miliyan biyu, kafin kotu ta bashi iskar ‘yanci.

Yanzu haka dai kotun ta dage cigaba da sauraron karar, zuwa ranar daya ga watan Disamba mai kamawa.

Mawakin, wanda tsohon sarkin Kano Muhammadu Sunusi na biyu, ya nada mukamin sarkin waka, an kama shi da fari tun a watan Satumbar shekarar 2019, bayan ya saki wata waka, ba tare da karbar izini daga hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ba.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!