Kiwon Lafiya
Abubuwan da ya kamata mai ciwon sikari ya riƙa ci – Dr Dije Kabara
Wata ƙwararriya likita a harkar cimaka ta ce yawan cin kifi da nama ga masu fama da cutar sikari na haifar musu da illa a jikin su.
Dakta Dije Kabara ta bayyana hakan ta cikin shirin Barka da Hantsi na Freedom Radio.
Likitar ta yi jawabin ne a wani ɓangare na bikin ranar masu fama da cutar sikari da ake gudanarwa a duk ranar 14 ga watan Nuwamban kowacce shekara.
“Masu fama da cutar sikari su guji cin jan nama da kuma kifi domin kuwa zai iya tsananta ciwon na su”.
Abubuwan da ya kamata masu fama da cutar su riƙa ci:
“Kamata yayi masu ɗauke da ciwon sikari su riƙa amfani da tsabar abinci ba tare da an cire musu dusar su ba kamar su Dawa, Gero, da kuma alkama” a cewar Dije.
Ta ci gaba da cewa “Mai fama da cutar sikari na buƙatar cin ganyayyaki da kayan marmari sannan ya riƙa shan ruwa akai-akai da kuma yawan motsa jiki.
Dakta Dije ta buƙaci masu cutar sikari su riƙa biyayya ga dokokin jami’an lafiya don kula da kan su.
You must be logged in to post a comment Login