Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Kwalara: Adadin rayukan da aka rasa sun zarta dubu 3

Published

on

Cibiyar daƙile yaɗuwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta ce, sama da mutane dubu 3, 449 ne suka mutu sakamakon cutar kwalara a 2021.

Rahoton na NCDC ya kuma bayyana cewa mutane sama da dubu ɗari da a hamsin da bakwai sun kamu da cutar a jihohi 32 har da birnin tarayya Abuja.

A cewar NCDC yaran da ke tsakanin shekara biyar zuwa 14 ne suka fi kamuwa da cutar tsakanin maza da mata, yayin da kashi 50 cikin 100 suka kasance maza ne.

Jihohin da aka samu bullar cutar kwalara a bana su ne Abia, Adamawa, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Ekiti, Enugu, Gombe, Jigawa, Kaduna, Kano.

Sai Katsina, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Sokoto, Taraba, Yobe, Rivers, Zamfara da kuma birnin tarayya Abuja.

NCDC ta kuma ce, daga ranar 1 ga watan Nuwamba zuwa 7 ga watan jihohi shida sun ba da rahoton sake ɓullar cutar guda 78 da suka hadar jihohin  Borno 32, Kebbi 20, Adamawa 19, Cross River 3, sai Ogun 2 da jihar Oyo 2

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!