Kiwon Lafiya
Abubuwan da yakamata ku sani game da ranar bada agajin jini ta Duniya
Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ware duk ranar 14 ga watan Yunin kowacce shekara a matsayin ranar bayar da kyautar jini ta duniya, da nufin godiya da kuma yabawa wadanda suke bayar da jinin su kyauta domin ceto rayukan jama’a.
Hukumar dai ta ware wannan rana ce tun a shekarar 2004 don yin karin bayani ga al’umma da kuma jami’an lafiya kan yadda mutane zasu rika bayar da tsaftataccen jini da kuma yadda jami’an lafiyar zasu alkinta shi.
Masana na ganin cewa kamata, ya yi a rika samun yawan masu bayar da kyautar jinni a kowannen yanki na duniya, ta yadda ba sai anyi tafiya mai nisa kafin samun jinin da za’a karawa mabukaci ba.
Haka kuma ranar na mayar da hankali wajen wayar da kan jama’a game da muhimmancin bayar da kyautar jini da kuma karfafar gwiwar masu niyyar yin hakan, baya ga sake bayani kan muhimmancin hakan.
A ranar, dai ana kuma horas da jami’an lafiya kan yadda zasu rika diban jinin mutane cikin tsafta da kuma alkinta shi, don karawa mabukata cikin gaggawa da nufin ceto rayukan su.
Wasu mutanen a nan Kano da muka zanta da su a nan Kano, sun bayyana mabanbantan ra’ayoyi dangane da bayar da kyautar jinni ko akasin hakan, inda wasu daga ciki sukace suna bayar da agajin jini ga mabukata, yayin da wasu kuma suka ce suna shirin bayarwa.
Da ya ke yiwa Freedom Radio jawabi kan bikin ranar, wani kwararren likita a sashen karin jinni na sibitin koyarwa na Aminu Kano Dakta Usman Abdullahi Makuku ya ce ‘baya ga ceto rayukan jama’a, wanda ya bada kyautar jini, yana samun kariya daga cututtukan da suka shafi na daji, ciwon zuciya da na hanta da kuma rage kiba.
Dakta Abdullahi Makuku ya kuma kara da cewa” akwai karancin mutanen da ke bada kyautar jini a wannan yankin, kuma ana samun masu bukatar jinin, sanadiyyar hadarin mota, haihuwa, tiyata da sauran su.
Sannan ya ce “Matasa ‘yan shekaru 18 zuwa 60 sune ya kamata su zage dantse wajen bada kyautar jini, ba wai sai ga ‘yan uwan su ba, a’a ga kowa ma don ceto rayukan jama’a.
Taken bikin na bana, shi ne bukatar da ke akwai wajen bayar da kyautar jini don ceto rayukan jama’a a duniya baki daya.
You must be logged in to post a comment Login