Labaran Wasanni
AFCON 2022: CAF ta sauyawa kasar Kamaru filin wasa
An sauya wa tawagar kwallon kafa ta kasar Kamaru filin da suke fafata wasannin gasar cin kofin kwallon kafar Afrika daga filin wasa na Olembe zuwa na Ahmadou Ahidjo da ke babban birnin kasar Yaounde.
An dai dauki matakin ne biyo bayan asarar rayuka da aka yi yayin da wasu ke kokarin shiga filin wasan a yayinda da Kamaru ke buga wasa da kasar Comoros a ranar Litinin 24 ga watan Janairun 2022.
Akalla mutune 8 ne suka mutu yayin da 38 suka jikkata bayan da wasu suka yi kokarin kutsawa cikin filin wasan na Olembe.
Za a ware minti daya a dukkanin wasannin gasar don nuna jimami ga wadanda suka mutu.
Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA da kuma hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF sun aike da sakon jaje ga iyalan wadanda suka mutu.
Shugaban CAF, Patrice Motsepe ya ziyarci wadanda ke jinya a asibitin Olembe a ranar Talata 25 ga watan Janairun 2022.
Shugaban ya ce alhakin CAF ne da kuma masu shirya gasar kan abin da ya faru tare da daukar matakai domin kauce wa sake aukuwar irin lamarin.
Filin Olembe da ke daukar ‘yan kallo 60,000, an takaita yawan wadanda za su shiga kallon wasanni a filin saboda annobar Korona.
You must be logged in to post a comment Login