Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Mutane 8 sun rasa ransu a wasan Kamaru

Published

on

A ƙalla mutane 8 ne suka rasa ransu sakamakon wani turmutsutsu da ya faru yayin wasan Kamaru da kasar Komoros a gasar cin kofin Afrika da ake gudanarwa a kasar.

An buga wasan ne a ranar Litinin 24 ga watan Janairun shekarar 2022.

An kuma buga wasan a katafaren filin wasan kasar mai suna Olembe dake Yaounde babban birnin kasar.

Kazalika rahotonni sun tabbatar da cewa mutane da dama ne suka samu raunuka yayin turmutsutsun da akayi.

Hukumar kwallon kafar kasar ta tabbatar da faruwar lamarin ta cikin wata sanarwa data fitar a safiyar yau Talata 25 ga watan Janairun 2022.

Ta kuma ce yanzu haka tana nan tana gudanar da bincike kan al’amarin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!