Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Qatar 2022: Najeriya ta kai zagayen karshe na neman tikitin buga kofin Duniya

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta kai zagayen karshe kuma na 3 na neman tikitin buga gasar cin kofin Duniya da za a gudanar a kasar Qatar a shekarar 2022.

Super Eagles dai ta tashi wasa canjaras da ci 1-1 da kasar Cape Verde a karawar da suka yi a ranar Talata 16 ga watan Nuwambar 2021 a filin wasa na Teslim Balogun dake jihar Legas.

Da wannan sakamakon Super Eagles ta ja ragamar rukuni na 3 da maki 13 bayan buga wasanni 6 da kowacce kasa ta yi, yayin da Cape Verde ta yi ta biyu da maki 11.

Liberia ce ta 3 da maki 6 da kuma Jamhuriyar Afirka ta tsakiya da maki 4 kuma ta karshe ta 4 a rukunin.

Yanzu haka Hukumar kwallon kafa ta Afirka (CAF) za ta raba kasashen da suka kai bantensu zuwa wasannin na gaba don fitar da biyar din za su wakilci nahiyar Afirka a gasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!