Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Afenifere da kabilar Igbo Ohaneze Ndigbo sun goyi bayan kalaman Osinbajo

Published

on

Kungiyar dattawan yarbawa zalla ta Afenifere da takwararta ta kabilar Igbo Ohaneze Ndigbo sun goyi bayan kalaman da mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo yayi a baya-bayan nan da ke cewa matukar aka ci gaba da tafiya a yanayin da ake a yanzu ba ko shakka kasar nan za ta iya rabuwa.

Haka zalika itama kungiyar Pan Niger Delta Forum ta al’ummar yankin kudu maso kudancin kasar nan ta ce tana tare da mataimakin shugaban kasa kan wannan ikirari.

Sai dai a bangare guda kungiyar dattawan arewa ta ACF taga baikin mataimakin shugaban kasa kan furta wannan kalami da ta ce ko kadan bai dace ace mutum kamar shine ya fada ba.

A cewar kungiyar ta ACF ba daidai bane ace mataimakin shugaban kasa yayi wannan kalami a wannan lokaci da kasar nan ke cikin tsaka mai wuya.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!