Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Buhari zai gina katanga a gabar ruwan kogin Kaduna

Published

on

Gwamnatin tarayya ta ce nan ba da dadewa ba, za ta gina Katanga a gabar ruwan Kogin Kaduna domin dakile matsalar ambaliyar ruwa da ke addabar al’ummar da ke makotaka da Kogin.

Mai rikon mukamin shugaban cibiyar kula da albarkatun ruwa ta kasa da ke Kaduna Dr. Martin Edufie ne ya bayyana hakan a jiya yayin zantawa da manema labarai.
Ya ce jama’a da dama sun rasa rayukansu yayin da dukiyoyi na miliyoyin nairori suka salwanta sakamakon ambaliyar ruwa wanda Kogin Kaduna ya janyo.

Dr Martin Edufie wanda ke jawabin a wani bangare na bikin ranar Koguna ta duniya, y ace gwamnati ta dau wannan mataki ne biyo bayan nazartar da kwararru su ka yi ga Kogin na Kaduna tsawon shekaru.

Saboda haka ya ce, nan gaba kadan ba da jimawa ba gwamnati za ta gina Katanga a gefen Kogin don hana ruwa haurawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!